Friday, December 5
Shadow

Ban ga Amfanin Zumudin Hadakatar ‘yan Adawar da El-Rufai yake yi ba, kamata yayi a bar Shugaba Tinubu ya nutsu yawa ‘yan Najeriya aiki kar a raba masa hankali>>Inji Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, yayi wuri ace an fara hadakar ‘yan Adawa dan zaben shekarar 2027.

Galadima ya bayyana hakane a hirar da Jaridar Punchng suka yi dashi inda yace Zumudin El-Rufai yayi yawa, yace ko da yake ba dan siyasa ban shiyasa amma yasa ba inda zashi.

Yace kamata yayi a bari shugaba Tinubu ya nutsu mayar da hankali wajan yiwa ‘yan Najeriya aiki.

Yace shi a yanzu ba zai ce komai akan mulkin Tinubu ba sai ya cika shekara biyu cif yana mulki kamin su duba suka yayi kokari ko akasin haka.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Duk masu min fatan in koma me kiba kamar yanda nake a baya, Ina Rokon Allah ya dora musu kibar>>Inji Hadiza Gabon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *