Saturday, December 13
Shadow

Bidiyo: Shugaba Tinubu ya isa jihar Anambra

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa jihar Anambra inda yake ziyarar aiki a yau, Alhamis.

Shugaban iya isa filin sauka da tashin jiragen sama na Chinua Achebe dake jihar inda ya samu tarbar gwamnan jihar, Charles Soludo da ‘yan majalisar jihar da sauran dattawan jihar.

Shugaba Tinubu kuma ya samu ya tsaya an masa taken Najeriya inda sojoji suka yi harbi sama dan girmamashi.

Bayannan kuma, Shugaba Tinubu ya shiga motar da aka tanada dan shi tare da Gwamnan jihar inda zai zarce dan fara kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta gudanar.

Karanta Wannan  Game da hatsarin da Jarumi Adam A. Zango ya yi, bayanai na nuna an samu wasu marasa Imani sun sace masa wayar sa da kuɗin sa har da ɗan cincin ɗin da mahaifiyar sa tayi masa guzuri da shi da sauran abubuwan amfani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *