Wednesday, April 8
Shadow

Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Arewacin Najeriya zasu gana a Kaduna saboda tattaunawa matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Rahoton yace hadimin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Misilli ne ya bayyanawa manema labarai na Punchng hakan inda yace gwamnan Gomben shine ya kira wannan taron a matsayinsa na shugaban Gwamnonin Arewan.

Yace idan dai ba an canja ba, a yau, Asabar ne za’a yi wannan taro a Kaduna kuma matsalar tsaron yankin ce babban abinda za’a tattauna.

Karanta Wannan  Dangote zai rage farashin man fetur dinsa daga Naira N865 akan kowace lita zuwa Naira N841 a Legas da sauran Jihohin Yarbawa, Sannan A Abuja da jihar Kwara da Edo, ma zai rage farashin man zuwa Naira 851 kan kowace lita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *