Wednesday, April 8
Shadow

Ban damu sai na koma Kujerar Gwamna ko ta halin kaka ba>>Gwamnan Jihar Rivers Simi Fubara

Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya bayyana cewa, bai damu sai ya koma mukaminsa na gwamna ba ko ta halin kaka.

Ya bayyana hakanne a wajan wani taron tunawa da dattijon jihar, Marigayi, Edwin Clark, inda masu jawabi da yawa da auka tashi suka soki dakatar dashi da aka yi da neman a mayar dashi kujerar Gwamna.

Fubara da ya hau wajan jawabi ya nesanta kansa da kalaman mutanen inda yace bai kamata a yi fito na fito kan lamarin ba.

Ya kara da cewa, suka san ko yana son komawa Kujerar gwamnan? Yace shi a yanzu ma ruhinsa ya bar gidan Gwamnatin jihar.

Karanta Wannan  An dakatar da bayar da làsìsìn Màkàmì irin su Bhìndìghà ga 'yan Najeriya dan su yi amfani da ita wajan kare kansu>>Inji Hukumar 'yansandan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *