
Shugaban kungiyar daliban Najeriya, Comrade Atiku Abubakar Isah, ya maka dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban gidan talabijin na kasa, NTA, da shugaban hukumar tsaron farin kaya, DSS a kotu inda yake neman a biyashi diyyar Naira Biliyan 38.3.
Ya kuma nemi a sakeshi daga tsaron da ake masa na tsawon kwanaki 14 wanda ya bayyana da cewa garkuwa ce aka yi dashi.
Hakanan ya kuma bayyana cewa yana neman kotu ta dakatar da bata masa sunan da ake yi, inda yace kuma tsaron da akw masa an take hakkinsa na walwala kamar yanda Kudin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowane dan kasa damar yi.
Dan haka yake neman kotun tarayya dake Abuja ta bi mai hakkinsa, ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, Ugwueze I. Oduegbu da R.O. Ifebhor.
An dai kama Kwamared Isa ne bayan da ya zargi Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da bashi Naira Miliyan 100 dan ya goyi bayan Tinubu amma yaki ya. Yace bayan hakane, Seyi Tinubu din yasa ‘yan iska suka bugeshi.
Saidai bayan da hukumar DSS ta kamashi, ya fitar da bayanin wanke dan shugaban kasar wanda daga baya aka yi tunanin tursasashi aka yi yayi hakan.