Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa game da yanda ake kirkiro Bidiyo na bogi na shugaban kasa dake nunashi a wani yanayi mara kyau domin ɓata masa suna

Ministan yaɗa labaran Najeriya Mohammed Idris ya gargaɗi ƴan ƙasar kan amfani da ƙirƙirarrun bidiyo domin nuna shugabannin ƙasar a wani yanayi mara kyau domin ɓata musu suna.

Jaridar The Nation mai zaman kanta ta ruwaito ministan yana cewa, “mun ga yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira ta hanyoyin da suka dace, da hanyoyin da ba su dace ba. Zai iya yiwuwa kana zaune a nan kawai sai wani ya yanko kanka ya ɗaura a wani jikin domin ɓata maka suna.”

“Muna ganin yadda ake juya maganar shugaban ƙasa, inda zai faɗa abu daban, amma sai a canja abin da ya faɗa. Ko kuma minista ya faɗa wani abu, sai a juya masa magana,” in ji shi.

Karanta Wannan  Matar Wannan mutumin ta ràsù a ambaliyar ruwan data faru a Mokwa jihar Naija, hakanan jaririnsa da 'yan uwansa 7 duk sun ràsù da kayan jikinsa kawai ya tsira

Ya ƙara da cewa suna duba lamarin sosai a matakin gwamnati, “musamman yadda za mu tsaftace kafofin sadarwa ba tare da tauye haƙƙin furta albarkacin baki ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *