
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyanawa ‘yan Najeriya cewa saukin rayuwa na nan kusa da bayyana.
Ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Bayo Onanuga inda yace kowane sako da lungu na kasarnan zai shaida alfanin tsare-tsaren gwamnatinsa wanda nan gaba kadan za’a fara gani.
Shugaba Tinubu yace a lokacin da ya hau mulki NNPCL baya iya kawo man fetur saboda bashi ya masa yawa yace amma a haka yayi kokari aka samu sauki.
Yace kuma ‘yan Najeriya da dama sun samu budin arziki a zamanin milkinsa.