Friday, December 5
Shadow

Akwai yiyuwar kara farashin Man Fetur a Najeriya saboda sabon harajin da Gwamnatin Tinubu zata sanya

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar kara farashin man fetur saboda wani sabon Haraji da Gwamnatin Tinubu zata kakabawa ‘yan Najeriya.

Ma’aikatar ayyuka ta kasa da majalisar wakilai ne suke son a fara karbar wannan haraji na amfani da titunan Najeriya.

Dan haka suke bayar da shawarar maimakon a rika karbar harajin kai tsaye, a rika karbarsa ta hanyar saka kudin a cikin kudin man fetur da ‘yan Najeriya ke saye.

Karamin Ministan ayyuka, Mohammed Goroyo ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta fara karbar wannan haraji musamman saboda gibin da gwamnati ke samu akan kudaden kula da titunan kasarnan.

Yace kudin da ake bukata dan kula da titunan Najeriya sun kai Naira Biliyan 800 duk shekara amma kudin da Gwamnati ke baiwa ma’aikatar basu kaiwa hakan.

Karanta Wannan  Wata budurwa mai suna Hafiza Rufaisa daga Gombe ta zama zakara a gasar karatun kur'ani ta kasa da aka kammala a Kebbi. Ta Samu kyautar motar, kudi, da sauransu

Dan hakane suke bukatar a fara karbar haraji daga hannun ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *