
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, (NRC) ta kara yawan zirgazirgan jirgin kasar dake Jigila daga Legas zuwa Ibadan.
Hakan na zuwa ne yayin da mutane ke ta tafiye-tafiye dan shagulgulan Sallah.
Me magana da yawun hukumar, Callistus Unyimadu ne ya bayyana haka inda yace jirgin dake Jigila tsakanin Warri-Itakpe shima zai yi aiki na musamman a ranar Alhamis.
Sannan yace jirgin Kaduna zuwa Abuja an kara mai yawan tarago.