Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi watsi da matakin bai wa kananan hukumomin kasar ‘yancin cin gashin kansu.
Buni ya bayyana ra’ayinsa ne jim kadan bayan kada kuri’arsa a zaben kananan hukumomi a mazabar sa da ke Buni Gari.
“Lokacin da na hau mulki a shekarar 2019, tunanina shi ne in ba kananan hukumomi cin gashin kai. Sai dai abin takaici shi ne kananan hukumomi shida cikin 17 na jihar Yobe ba sa iya biyan ma’aikata albashi.
“Saboda haka, hikimar da ke tattare da wannan asusun hadin gwiwa, wanda ya hada da kokarin kananan hukumomi tare da jihar tare da hadin gwiwa wajen aiwatar da wasu ayyuka, ra’ayi ne da aka samu daga wadannan gazawar,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana fatansa game da makomar cin gashin kan kananan hukumomi a Najeriya.
“Dimokradiyyarmu tana girma, kuma za a magance wannan batu ba tare da wata matsala ba,” in ji Buni.
Yunkurin da ake yi na kwato kananan hukumomi daga kangin asusun hadin gwiwa ya kasance batun tattaunawa da jama’a, inda da dama ke kallon matakin a matsayin mataki mai kyau, yayin da wasu ke da ra’ayi daban-daban.
An yi ta yada cewa kotun kolin Najeriya ta umurci jihohi da su kare kan su kafin ta yanke hukunci kan lamarin da ke gabanta.
Daga: Abbas Yakubu Yaura