Thursday, December 25
Shadow

An kaddamar da shafin Yanar gizo na masoya Shugaba Tinubu, da ke da ra’ayin sake zabensa a 2027 duk wanda ke da ra’ayi yana iya zuwa yayi rijista

Kungiyar masoya shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sun kaddamar da shafin yanar gizo na wadanda kw da ra’ayin sake zaben shugaban kasar a shekarar 2027.

Kungiyar me suna the BAT Ideological Group ta bayyana cewa, ta yi hakanne dan hada bayanan masoya shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da wanda suke son sake zabensa.

Kungiyar tace kuma hakan zai saukaka maganar ace sai mutum ya je Abuja dan za’a yi meeting ko dan zai yi rijista.

Tace kuma hakan zai saukaka mata yada manufar shugaban kasar ga al’umma.

Shugaban kungiyar, Bamidele Atoyebi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Bashin da Shugaba Tinubu zai ciwo zasu sace ne shi da mutanensa ba dan Talakawa bane>>Inji Malam

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *