
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata korkiro da kamfanin Karafa na Ajakuta.
Ministan karafa, Shuaibu Abubakar Audu, ne ya bayyana hakan inda yace Gwamnatin tuni ta shiga mataki na gaba wajan farfado da kamfanin.
Ministan ya bayyana hakane a yayin da yake ganawa da wasu ‘yan jam’iyyar APC yayin da suka kai masa ziyara a gidansa dake jihar Kogi.
Yace tuni Gwamnatin ta shiga yarjejeniya dan farfado da kamfanin sannan tana kokarin jawo hankalin masu zuba hannun Jari musamman daga kasar China dan su zo su zuba jari a kamfanin dan farfado dashi.
Yace suna aiki me kyau kan lamarin kuma zasu tabbatar sun bayar da sakamako me kyau.