
Jihohi 4 daga cikin 6 na yankin Arewa maso gabas, watau jihohin Taraba, Adamawa, Borno da Yobe sun fada duhu bayan da wutar lantarkinsu ta lalace.
Da misalin karfe 10:00 am na safiyar ranar Talata, 10 ga watan Yuni ne wutar ta samu matsala. Kuma ana tsammanin sai nan da Ranar Asabar, da misalin karfe 5:00 pm za’a gyara wutar.
Lamarin ya taba harkokin kasuwanci a jihar inda dama saidai su koma amfani da janareta, ko Sola wanda kuma basu da wannan saidai su hakura.
Kamfanin Yola Electricity Distribution Company, YEDC yace dauke wutar ya zama dole dan a inganta injinan ko yanayin samar da wutar.
Kamfanin ya bayyana jin dadin hakurik mutane da hadin kan da suka bayar kan wannan aiki.