
Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fasa jawabin da ya shirya yiwa ‘yan Najeriya da safiyar ranar ‘yanci.
Rahotan yace, maimakon haka, shugaban zai yiwa ‘yan Najeriya jawabi ne daga zauren majalisar tarayya.
Shugaba Tinubu zai halarci zauren majalisar tarayya dan baiwa wasu ‘yan majalisar kyautar girmamawa.