Friday, December 5
Shadow

Kotun daukaka kara ta dakatar da shirin kwacewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele kadarorinsa inda tace kudin da yake dasu zasu iya sayen kadarorin

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{“square_fit”:1},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:true,”containsFTESticker”:false}

Kotun daukaka kara ta dakatar da hukuncin kotun baya na kwace wasu kadarorij tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.

A ranar April 9, 2025 ne kotun ta yanke wanan hukunci inda tace kadarorin da aka kwace a baya na Emefiele wadanda suka hada da gidaje da filaye a Legas da jihar Delta kudaden da yake dasu ta hanyar halal zai iya siyen fiye da wadannan kadarorin.

A ranar November 1, 2024 ne Babbar kotu a Legas ta kwace kadarorin na Emefiele bayan da EFCC ta shigar da kara tana cewa tana zargin kadarorin an samesu ne ta hanayar sata.

Saidai Mai shari’a na kotun daukaka kara,Abdulazeez Anka, ya bayyana cewa kudaden da Emefiele ya samu na aikin da yayi da bankin Zenith da CBN zasu iya sayen fiye da wadannan kadarorin.

Karanta Wannan  Fina-Finan da 'yan Najeriya ke kallone yasa mutane da yawa ke son yin kudi dare daya>>Inji Matar Shugaban kasa, Remi Tinubu

Anka ya kara da cewa, kudin sallamar aiki na Emefiele bayan da ya zama shugaban bankin Zenith sun kai 1,750,000,000, sannan yana da hannun hari a bankin da darajarsa ta kai Naira 500,000,000, hakanan mai shari’ar yace albashin Emefiele a matsayin gwamnan CBN duk shekara yana daukar naira N350,000,000 sannan shekaru 10 yayi a matsayin gwanan na CBN.

Yace dan haka kadarorin da aka kwace na Emefiele da sunan cewa ana zargin na sata ne, Albashinsa zai iya sayen abinda ya fisu.

Dan haka kotun tace a sake yin shari’ar dan samun tabbatattun hujjoji cewa kadarorin na Emefiele na satane ba da kudin halal ya sayesu ba.

Karanta Wannan  Mata basu son yin aiki da mata a matsayin oganninsu a Ofis shiyasa ake samun irin Mutuminnan na nasar Equatorial Guinea masu yin lalata dasu>>Sanata Shehu Sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *