
Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, banda jam’iyyarsa ta AAC duk sauran jam’iyyun APC ce take juyasu.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV ranar Lahadi.
Sowore yace mafi yawancin sauran jam’iyyun an kirkiresune kawai dan a yaudari ‘yan Najeriya.
Yace Jam’iyyar AAC wadda ya kirkiro a shekarar 2018 ce kawai jam’iyyar adawa ta gaskiya.
Sowore yace mafi yawanci APC na baiwa wadannan sauran kananan jam’iyyun kudi nw idan zabe yazo su musu aiki.