
Hukumar kididdi ta Najeriya, NBS tace farashin kayan masarufi ya sauka da kaso 22.97 a watan Mayu idan aka kwatanta da na watan Aprilu da yake kaso 23.71 cikin 100.
NBS ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ranar Litinin.
Idan aka kwatanta da shekarar data gabata, farashin kayan masarufin na yanzu yana kan kaso 10.98% ne cikin 100 wanda shima za’a iya cewa ya sauka idan aka kwatantashi dana shekarar 2024 wanda yake akan maki (33.95%).
Yawanci ana tattara farashin kayan abinci ne dana Haya dana ababen hawa wajan fitar da wadannan alkaluma.