
Kudin Naira kusan za’a iya cewa ya rasa darajarsa baki daya a cikin shekaru 65 da suka gabata.
Bincike ya nuna cewa Naira 100 a shekatar da aka baiwa Najeriya ‘yanci watau 1960 daidai take da Naira Miliyan 1.1 a yanzu.
An alakanta faduwar darajar Nairar da hauhawar farashin kayan masarufi da Karya darajar Nairar da kuma rashin iya gudanar da tattalin arziki.
Hakan dai ba karamin ci baya bane ga Najeriya.
An samo wadannan bayanai daga World Data ne.