Friday, December 5
Shadow

Ministan Tsaro, Badaru Ya Wakilci Tinubu A Taron Nazari Kan Kundin Tsarin Mulki

Ministan Tsaro, Badaru Ya Wakilci Tinubu A Taron Nazari Kan Kundin Tsarin Mulki.

Mai girma ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, CON, MNI, a yau Litinin, 16 ga watan Yuni, 2025, ya wakilci mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron nazari kan kundin tsarin mulki a tsakanin masu ruwa da tsaki kan dokoki dangane da tsarin tsaron ƙasa, wanda aka gudanar a cibiyar daƙile ayyukan ta’addanci da ke ofishin babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Abuja.

Taron wanda kwamitin nazari kan kundin tsarin mulkin ƙasa na majalissar wakilai ya shirya tare da haɗin gwiwar ofishin babban mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro da sauran hukumomin tsaro, ya samu halartar manyan jami’an tsaro da ƙwararrun masana kan dokoki da tsare-tsare.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Kalli Hotunan Mahaddacin Qur'ani da 'yan Bìndìgà suka yi garkuwa dashi da iyayensa a jihar Katsina

A yayin taron, ministan tsaro, Badaru, ya gabatar da jawabin shugaban ƙasa na buɗe taron a madadin shugaban ƙasar.

Daga Safwan Sani Imam
Personal Assistant ( New Media ) to the Honourable Minister of Defence.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *