Friday, December 5
Shadow

Idan baka hada kai da shugaban kasa Tinubu ba, Jihar Zamfara zata tafka Asara>>Sanata Orji Kalu ya gayawa Gwamna Lawal Dare

Sanata Orji Kalu ya baiwa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare shawarar ya gyara alakarsa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ya bayyana hakane a ziyarar da ya kai jihar ta Zamfara ya kaddamar da Makarantar Kimiyya da fasaha da kuma sabuwar ma’aikatar mata ta jihar Zamfara da aka gina.

Sanata Kalu yace alaka me kyau da shugaban kasa, zata sa jihar Zamfara ta kara samun ayyukan ci gaba.

Ya bayyana cewa, ba wai sai Gwamna Dare ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC amma alaka me kyau tsakaninsa da shugaban kasa, zata taimaka sosai wajan ci gaban jihar ta Zamfara.

Karanta Wannan  Anata ta cece-kuce saboda babu mace ko daya data halarci wajan sakawa kasafin kudin 2025 hannu da shugaba Tinubu yayi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *