Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a harin Jihar Benue

Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi a al’ummar Yelwata da ke ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benue, ranar 13 ga Yuni, 2025.

Egbetokun ya ce an tabbatar da mutuwar mutum 47 a cikin harin, yayin da wasu 27 kuma suka jikkata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Rundunar ‘yan sanda ta ce an kuma kashe wasu biyu daga cikin ‘yan harin a ranar da lamarin ya faru.

Egbetokun ya ce an tura jami’an tsaro domin bin diddigin lamarin, kuma daga baya an kama wasu manyan masu hannu biyu-biyu a kisan wanda hakan ya kai ga kama karin mutum bakwai.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa, an shigar da karar neman tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu daga kan kujerarsa saboda cin zalin 'yan kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *