Friday, December 5
Shadow

Gajartace tawa El-Rufai yawa shiyasa ya ke ta soki burutsu>>Inji Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gajarta ce tawa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yawa shiyasa yake ta soki burutsu.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.

El-Rufai a wata hira da aka yi dashi yace a wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da suka gudanar sun gano cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai ci zaben shekarar 2027 ba.

Saidai Onanuga yace babbar matsalar El-Rufai shine shi a ko da yaushe yana son ya nuna yafi sauran mutane.

Yace El-Rufai bashi da biyayya inda yawa mutane da yawa a baya ciki hadda wansa wanda tsohon soja ne.

Karanta Wannan  Kai ma ka taimaka wajen ƙara talauci a Najeriya’>>Gwanati ta mayarwa Peter Obi Martaninkan cewar da yayi talauci ya karu

Yace kuma makaryaci ne sosai wanda ke yin abubuwa yawanci dan kawai amfanin kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *