
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ce gatan ‘yan Najeriya inda yace kada su saurari masu cewa zasu kayar dashi zabe a 2027.
Shugaban yace ‘yan adawar dake hada kai da zummar kayar dashi zabe ‘yan gudun hijirar siyasa ne.
Shugaban ya bayyana hakane ranar Laraba a yayin ziyarar da ya kai jihar Nasarawa ta kwana daya.
Ya yabawa gwamnan jihar, Abdullahi Sule kan aikin da yakewa mutanen jiharsa inda yace zai tallafa masa da dukkan wani aikin ci gaba da zai kawo.