
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, hukumar ‘Yansandan farin kaya DSS ta kama masu garkuwa da mutane 6 da suka dawo daga aikin Hajji a filin sauka da tashin jiragen saman jihar.
An kamasu ne da misalin karfe 3:40am kamar yanda wata majiya ta gayawa majiyarmu.
Wadanda aka kama din mata 3 ne maza 3 kamar yanda rahoton ya tabbatar.
An kama su ne da daren ranar Talata.
Zuwa yanzu dai ba’a fitar da bayanai kan sunaye ko hotunan wadanda aka kama din ba.
Ko da a watan Mayu da ya gabata dai an kama wani me garkuwa da mutane me suna Sani Galadi da ke shirin tafiya zuwa aikin Hajji.