
Kungiyar Gwamnonin Najeriya wadanda aka zaba karkashin jam’iyyar APC sun bayyana jin dadinsu da saukar Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar.
Kungiyar ta bayyana hakane bayan taron data gudanar a birnin Benin City na jihar Edo inda ta fitar da sanarwa ta bakin shugabanta, Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma.
Kungiyar tace jam’iyyar APC itace kan gaba wajan karfi har yanzu kuma ba rikici bane yasa Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar ba.
Ya sauka ne saboda garambawulnda tsaftace jam’iyyar da ake yi dan gobe.