
Yayin da manyan mutanen jihar Kano suka hallara a Madina wajan jana’izar Marigayi Aminu Dantata, ana ta daga wuya dan ko za’a hango Kwankwaso amma ba’a ganshi ba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawagar Gwamnan Jigawa da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero zuwa jana’izar.
Da yawa sun yi tsammanin za’a ga Kwankwaso a cikin tawagar amma ba’a ganshi ba.
Hakan yasa ake ta cece-kuce akai.
Wasu dai na ganin zuwan Abba Gida-Gida ya isa ya wakilci Kwankwaso a wajan jana’izar, inda wasu ke ganin ya kamata ace shima Kwankwaso na wajan.