
Basaraken kauyen Yashikira dake karamar hukumar Baruten, a jihar Kwara, Amb (Dr) Alhaji Umar Sariki Usman, ya bayyana cewa da an kai kusu hari sai sojoji su tsere su barsu.
Basaraken ya nuna damuwa kan yanda sojojin da aka kai musu basa iya basu kariya.
Ya bayyana cewa, duk da alkawarin gwamnati na kai karin jami’an tsaro amma har yanzu ba’a kai ba.
Yace ‘yan bangansu da basu da makamai masu kyau sune suke fuskantar ‘yan Bindigar.
Yace sojojin da aka kai musu basu da kwarewar aiki kuma basu da kayan aiki masu kyau.