
Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Garba Shehu ya kare salon mulkin shugaba Muhammad Buhari.
Malam Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise TV, inda ya amince da cewa duk da wani lokacin ana bayyana shugabancin Buhari da mai jan ƙafa amma ya ce hakan na faruwa ne sakamakon ƙoƙarinsa na bin ƙa’ida wajen aiwatar da al’amura a ƙoƙarinsa na sauyin da yake yi daga mulkin soji zuwa na farar hula.
Sai dai kuma tsohon mataimakin na Buhari, ya ce ƴan Najeriya ba su da haƙuri kasancewar suna son sha yanzu magani yanzu ko da kuwa za a saɓa ƙa’idojin dimokraɗiyya.
“Yana da jan ƙafa? E, shi ma da kansa ya kan yi barkwanci dangane da hakan. Kuma ya yawan faɗin hakan lokacin da ya hau mulki a matsayinsa na soja, yana yin abun da ya ga damar yi sannan ya bayar da umarnin a kama da rufe mutane. To amma yanzu a matsayinsa na shugaban mulkin dimokraɗiyya, akwai buƙatar bin ƙa’idojin doka kafin aiwatar da al’amura.” In ji Malam Garba Shehu.