
Hukumar kula da sararin samaniya da yanayi ta kasa, The Nigerian Meteorological Agency ta yi gargadin cewa, Jihohi 20 na Najeriya na fuskantar Ambaliyar ruwa.
Saidai hakan na zuwane bayan da ake sukar gwamnatocin jihohi saboda rashin sanin ya suka yi da kudin shirin ambaliyar ruwa Har Naira Biliyan 620 da aka basu.
Rahoton yace duk da wadanan kudade jihohi da yawa basu shiryawa zuwan ambaliyar ruwan ba.
Jihohin da ambaliyar ruwan zata fi kamari sune Sokoto, Kaduna, Zamfara, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Jigawa, Adamawa, Taraba, Niger, Nasarawa, Benue, Ogun, Ondo, Lagos, Delta, Edo, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.
Hukumar tace mutanen wadannan jihohi idan zai yiyu su canja gurin zama kuma a gyara makwararun ruwa sannan a kashe wuta da gas yayin ambaliyar ruwan.