
Gwamnatin tarayya tace shekaru 16 ne mafi karanci na shiga jami’a.
Hakan ya fito ne daga bakin Ministan Ilimi, Tunji Alausa. Ya bayyana hakanne a Abuja wajan taron karawa juna sani na hukumar JAMB.
A shekarar 2024 dai, Tsohon Ministan Ilimin, Tahir Muhammad ya saka shekaru 18 a matsayin shekaru mafi karanci na shiga jami’ar.
Saidai bayan nada Tunji Alausa, ya canja zuwa shekaru 16.