Friday, December 5
Shadow

Buhari mutum ne me sin Addini>>Inji Sheikh Mufti Menk

“Buhari ba ya wasa da Sallah”- Mufti Menk.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Malamin addinin Muslunci, Sheikh Mufti Menk ya baiyana rasuwar tsohon shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari a matsayin abinda ya sanya ya zubar da hawaye.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mufti Menk ya suffanta Buhari da gwarzo kuma jarumi kuma shugaba mai gaskiya.

A cewar Menk, Buhari ba ya wasa da Sallah kuma mutum ne da ya yi wa ƙasa hidima iya iyawar da.

“Rasuwar wani gwarzo, tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari – Allah ya ji kansa – ta sa na zubar da hawaye!

“Mutum ne mai gaskiya, wanda ba ya wasa da sallah, kuma mai tsananin ladabi da biyayya ga addininsa. Ya yi wa mutanensa hidima gwargwadon iyawarsa. Ya yi shura wajen riko da amana.

Karanta Wannan  Mahaifiyarka ta zabi lokacin da ya dace ta rigamu gidan gaskiya, ta koma ga Allah>>Akpabio ya gayawa

“Lalle yana daya daga cikin wadanda suka sa na fara ganin ‘yan Najeriya a wata kyakkyawar fuska.

“Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya ɗaukaka matsayinsa a Aljanna Firdaus. Ameen.

“Allah ya sauƙaƙa wa iyalansa, abokansa da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya,” in ji Menk.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *