
Dan tsohon shugaban kasa, Yusuf Buhari ya gabatar da jawabi a zaman majalisar zartaswa da aka gudanar a yau a fadar shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu inda akawa Marigayi, Muhammadu Buhari Addu’a.
Yusuf Buhari yace suna godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa da matansu da shuwagabannin majalisar tarayya da suka nuna damuwa da kuma addu’o’in da sukawa mahaifin nasu.