
Me martaba Sarkin Daura, Umar Farooq Umar ya bayyana cewa a mazabar Daura shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zabinsu a zaben 2027.
Ya bayyana hakane yayin da matar shugaban kasar, Oluremi Tinubu ta je fadarshi dan mika sakon ta’aziyya gareshi.
Uwargidan tsohon shugaban, A’isha Buhari ce ta jagoranci tawagar data hada da ministoci da matan gwamnoni da matar shuwagabannin tsaro zuwa fadar sarkin Dauran inda akawa Buhari addu’a.
Hakanan sun je kabarin Buharin inda a camma aka masa addu’a.
Sun kuma kaiwa mamman Daura ziyara a gidansa inda a camma suka mai gaisuwa.