Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan Najeriya sun shirya yin zanga-zangar yunwa da rashin abinci.
Zasu yi zanga-zangar ne ranar 12 ga watan Yuni.
Mutanen zasu yi hakanne a karkashin gamayyar kungiyoyi da yawa inda suka ce gwamnatin Tinubu ta kawo wahala a Najeriya.
Sun koka da cewa, da yawan ‘yan Najeriya basa iya cin abinci.