Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero, ya umarci hakimai a jihar Kano da su shigo cikin birnin na Kano domin fara shirin hawan sallah babba.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da galadiman Kano Alhaji Abba Sunusi ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta kuma buƙaci hakiman da su shigo cikin Kano da dagatansu, mahaya da kuma dawakansu.
Menene ra’ayinku?