Kalli Bidiyo: Tabbas Allah na yafe hakki ko da me hakkin bai yafe ba, Albanin Gombe ya goyi bayan Sheikh Asadussunnah
by Bashir Ahmed
Malamin Addinin Islama da akewa lakabi da Albanin Gombe ya goyi bayan Sheikh Musa Asadussunnah kan ikirarin da yayi cewa ko da wanda aka zalinta bai yafe ba Allah na yafewa.
Sheikh Musa Asadussunnah ya bayyana cewa Allah na yafe hakki ko da me hakki bai yafe ba inda take magana akan masu cewa Basu yafewa Buhari ba.
Shima dai Albanin Gombe yace Annabi yace idan aka samu wanda basa shirka mutum 40 sukawa mutum Sallah, Allah yana yafewa matacce.