
Rahotanni sun bayyana cewa, Dangote ya sauka daga shugabancin kamfanin sa na Siminti inda zai mayar da hankali kan matatar mansa.
Me magana da yawun kamfanin nasa na Siminti, Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan.
Yace an nada Emmanuel Ikazoboh a matsayin sabon shugaban kamfanin simintin na Dangote.
Yace hakanan an baiwa Hajiya Mariya Aliko Dangote mukamin daga daga cikin masu gudanarwa na kamfanin.