
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya fito yayi raddi ga ‘yan Izala musamman na Jos.
Yace suna wa har matattu Kazafi.
Malam ya kawo misalai a karatunsa inda yace wai sunce lokacin da za’a bashi limanci a Abuja, sai da aka kira surukinsa amma ya bayar da shaida mara kyau akansa.
Hakanan dan Malamin ma ya fito yayi raddi ga Izalar Jos inda yace a baya har so suka yi su kashe mahaifin nasu Sheikh Nura Khalid.
Yace amma ya tsallake rijiya da baya.