Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Gaskiya da Wahala a samu kamar babanmu wajan kula da gida, Sannan mutum ne me tauhidi>>Inji Diyar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, watau Zahra Buhari

Diyar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, watau Zahra Buhari ta bayyana cewa, mahaifinsu ya iya rikon gida.

Tace mutum ne wanda suke kallonshi a matsayin dama haka Namiji ya kamata ya kasance.

Tace yana musu sutura, abinci, kuma yana kula dasu yanda ya kamata.

Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita bayan rasuwar mahaifinta inda aka tambayeta ta fadi wasu abubuwa akan mahaifinta wanda ba kowane ya sani ba.

Ta kara da cewa mutum ne me Tauhidi.

A lokacin da ya rasu a Landan an ga yanda Zahra Buhari ta kwalla ihu akan titi.

Karanta Wannan  Kai baka san irin kwamacalar dana iske bane da kake sukata akan cire tallafin man fetur, dolene in cireshi gaba daya>>Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya mayarwa da Atiku Martani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *