Wani magidanci a jihar Abia ya danne matarsa ya kwakule mata idanuwa bisa niyyar yin kudin sihiri.
Mutumin me suna Lawrence Uzor yana sana’ar Alminiyum ne.
Lamarin ya farune a Adiele Estate dake karamar hukumar Umueze Ibeku in Umuahia ranar Asabar 24 ga watan Augusta.
Mutumin dai yayi amfani da wuka ne ya kwakule idanun matar tasa yayin da take bacci.
Me gidansu data ji ihu cikin dare ta yi kokarin kai dauki itama ya illatata amma daga baya an kamashi, inda su kuma wanda suka jikkata an garzaya dasu zuwa Asibiti.
Uwar gidan gwamnan jihar, Mrs Priscilla Otti ta bayar da tabbacin daukar matakin da ya dace akan lamarin inda ta bayar da kudi dan a kula da wadanda suka jikkata.