Friday, December 5
Shadow

Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a garin Yauri na jihar Kebbi a wani mataki na bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa.

Matakin na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami’an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin jihar Kebbi a ranar Alhamis.

Tawagar ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu – wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.

Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne domin faɗaɗa ayyukanta zuwa sauran yankunan ƙasar, musamman domin samar da tsaro a kan iyakokin ƙasar na tudu da na ruwa domin magance ayyukan ɓata-gari a kogin Niger.

Karanta Wannan  ALLAH SARKI: Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouq, Ta Fashe da Kuka Yayin Taron Addu’a na Musamman Ga Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari

“Duk da irin muhimmanci da kogin Niger ke da shi wajen haɓaka ayyukan noma da samar da lantarki da kamun kifi da sauran sana’o’i, sannu a hankali ɓata-gari na mafani da shi wajen aiwatar da muggan ayyukansu”, in ji Nwatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *