
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan Najeriya da suka yi rijista da jam’iyyar ADC sun kai mutane 800,000.
Hakan na zuwane daga bakin kakakin jam’iyyar na Jihar Rivers, Luckyman Egila, inda yace ADC ta zama Amarya a jiharsu dan manyan mutane sai tururuwar shiga cikinta suke.
Ya bayyana cewa, daga cikin wadanda suka shiga jam’iyyar ta ADC akwai tsaffin Gwamnoni da tsaffin ‘yan majalisar tarayya da sauransu.