
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya goyi bayan fatawar da Sheikh Ibrahim Maqari ya baiwa tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin.
Sheikh Nura Khalid yace akalla dai an rabasu da wani abu daga cikin miyagun abubuwan da suke.
Yace kuma idan zasu ci gaba da sauraren wa’azi zama su daina baki daya.
Ya bayyana cewa, Sheikh Maqari yayi amfani da Hikima irin ta masu wa’azi wajan bayar da fatawar.
Gfresh dai ya je gaban Maqari inda ya nemi fatawa kan Bidiyon da suke yi da iyalansu.
Sai Sheikh Maqari ya bashi fatawar cewa, idan zasu rika aika sakon da’awa hakan ba matsala bane.