
Rahotanni daga kasar China na cewa, masana kimiyya na kasar na aiki tukuru dan ganin sun samar da Mutum-Mutumi, Robot da zai rika daukar ciki yana haihuwar jariran gaske.
Kafar The Telegraph tace kamfanin fasaha na kasar China me suna Kaiwa Technology na kokarin samar da robot din wanda zai zo da mahaifa da zata rika haihuwar jariraan mutane.
Nan da shekarar 2026 ne za’a kammala hada robot din wanda farashinsa zai kai Fan £10,000.