Wednesday, April 8
Shadow

Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa masu saka hannun jari na kasar Brazil cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da ake aiwatarwa a Najeriya suna samar da ingantattun sakamako, inda ya yi ikirarin cewa “ba a sake samun cin hanci da rashawa ba” tun bayan da ya hau kujerar shugaban kasa.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Litinin tare da ministoci daga kasashen biyu da kuma mambobin kungiyar kasuwanci ta Brazil, inda ya sake jaddada shirye-shiryen Najeriya na karfafa hadin gwiwa a bangaren fasahar zamani, samar da abinci, masana’antu da makamashi.

Karanta Wannan  Sabbin Bidiyon Mutuniyar Soja Boy, Iftihal Madaki, tsohuwar me saka Hijabi sun dauki hankula sosai

Tinubu ya bayyana tattalin arzikin Najeriya a matsayin “wata babbar kasuwa mai dimbin damammaki da kamfanonin Brazil ba su taba cin moriyarta ba.”

Ya amince cewa gyare-gyaren da ya fara aiwatarwa “sun kasance masu zafi a farko, amma a yau sakamakon yana bayyana.”

“A hankali jama’a suna fahimta. Muna da karin kudade a cikin tattalin arziki, kuma babu cin hanci da rashawa.”

Don nuna gaskiya da adalci, ya yi nuni da Babban Bankin Najeriya (CBN), inda ya ce: “Ba sai ka san wani ba kafin ka samu kudin waje da kake bukata. ‘Yan wasa da karairayi sun fita daga kasuwa. A kasuwar kudin mu, kofa a bude take ga dukkan kasuwanni.”

Karanta Wannan  Hotuna: Wannan kyakkyawar budurwar na neman mijin aure, tace a taimaketa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *