
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya da kasar Brazil sun kulla huldar kasuwanci data hada da Kudi, Harkar lafiya, da sufuri da kuma huldar diflomasiyya.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace a yanzu sun kulla huldar tashin jirage daga Najeriya zuwa kasar Brazil Kai tsaye.
Sannan akwai maganar kimiyya da fasaha da sauransu.