Friday, December 26
Shadow

Kalli Bidiyon yanda Babban dan siyasa, Shaibu Gwanda Gobir ya fallasa yanda ake sace man fetur a Najeriya fiye da wanda Najeriyar take samu

Dan siyasa, Shaibu Gwanda Gobir ya fallasa yanda yace Turawa ke satar danyen man fetur daga Najeriya fiye da wanda Gwamnatin Najeriyar ke samu.

Yace ya je inda ake hako man fetur amma aka hanashi karasawa ainahin inda ake fitar da man.

Yace shugaban wajan ya kawo masa makudan kudade yace ya karba ya hakura da maganar zuwa ya gani dan kuwa idan yace sai ya je ya gani za’a iya kasheshi.

Yace baturen dake aiki a wajan ya gaya masa cewa ko turawa nawa za’a kashe sai an sake kawo wasu saboda irin man fetur din da suke samu ta barauniyar hanya ya kai kusan ganga Miliyan 5 a yayin da Gwamnati kuma ke samun ganga Miliyan 2.

Karanta Wannan  Gwamnatin Kano na da kudin da ta fi Karfin Haka: Shehu Sani yace Naira Miliyan daya da Gwamna Abba yace a baiwa kowane iyalan 'yan kwallon Kano da suka ràsù a hadarin mota ta yi kadan
https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1960465128756851014?t=jRQzQrw4Rr2PfNmTvTutxA&s=19

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *