Friday, December 5
Shadow

Allah Sarki: Kalli bidiyon Yanda wannan malamin ya sassauta lafazi akan Rasuwar Habu Dan Damisa, Yace Lamarinshi na gurin Allah a daina munana masa zato, bayan da a baya yayi wa’azi me kaushi sosai akan Dan Damusa amma yaran Dan Damusa suka gargadeshi

Wannan malamin ya fito ya sassauta lafazi akan wa’azi me kaushi da yayi a baya akan rasuwar dan daba, Habu Dan Damisa na Kaduna.

Malam a yanzu yace, a dauna munana zato akan dan Damisa inda yace lamarinsa na ga Allah, in yaso ya azabtar dashi in yaso ya yafe masa.

@ib_yusuf_muhd_sambo

DAN DAMISA… Duniya kenan, Wanda baizo ba ma tana jiransa. Ai da Babu mutuwa da shari’a, da wasu sunxci banza. Allah sa muyi karshe Mai kyau

♬ original sound – Ibrahim yusuf muh’d Sambo

Saidai da yawa sun ce malamin tsoro yaji kada yaran dan Damisa su illatashi ko kumama aikashi kiyama.

Karanta Wannan  Kalli hotunan yanda ake ginin tashar jirgin kasa ta zamani a Kano

A baya dai malam yayi Allah wadai da irin rayuwar dan Damisa inda ya kushe harkar daba duk da dai wa’azi ne yayi.

@ib_yusuf_muhd_sambo

HABU DAN DAMISA: Matashin Da Ya Yi Kàurin Sunà A Harkaŕ Daba A Yankin Tudun Wada Da Kewaye A Jihar Kaduna Ya Gamu Da Ajalinsa Saidai mutuwarsa ta raba hankulan jama’a, inda wasu ke jimami wasu kuma na mùrñà, duba da yadda ya aďdabi jama’à. Ko a wani bidiyo da aka nuno kusan yara ne zalla suka yi jana’izarsa.

♬ original sound – Ibrahim yusuf muh’d Sambo

Akwai wani matashi da ya fito yayi zagezage akan malamai, sannan ko a kasan Bidiyon malam an ga yanda ake mayar masa raddi masu zafi.

Karanta Wannan  Dangote ya dakatar da shirin rage farashin man fetur bayan da ya gano wasu 'yan kasuwar man na cutarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *