
Matashiya da jami’an hukumar shige da fici na kasa Immigration suka tare suka bukaci ta nuna musu takardar zama dan kasarta ta nuna amma duk da haka aka bukaci da bayar da wayarta ko kuma ta je ta ga ogansu ta dauki hankula.
A Bidiyon ta da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta, an ji tana fadin cewa ba za’a karbar mata waya ba sannan kuma ba zata je ta ga shugabansu ba.
Lamarin dai ya jawo mata yabo sosai duk da an samu wasu dake ganin cewa abinda ta yi bata kyauta ba.