Friday, December 5
Shadow

Duk budurwar da Saurayi ya aika mata da kudin mota da niyyar cewa ta je ta sameshi amma ta ki zuwa zata iya fuskantar hukunci, Hukumar ‘yansandan Najeriya ta gargadi ‘yan mata

Hukumar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Rivers sun gargadi ‘yan mata dake karbar kudin mota a hannub samari da niyyar cewa zasu je a hadu amma su ki zuwa.

Hukumar tace hakan laifi ne na zamba cikin aminci da kuma samun kudi ta hanyar karya, hukumar tace idan saurayi ya shigar da kara, za’a iya hukunta budurwar.

Kakakin ‘yansandan jihar, Grace Iringe-Koko ce ta bayyana hakan a shafinta na X inda ta jawo hankalin mutane su daina neman kudi ta hanyar da bata dace ba.

Karanta Wannan  Da Dumisa: Dangote zai fara hako danyen ma Fetur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *